Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta gindaya Wa Masu Shirin Zanga-Zanga Wasu Sharudda

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar da su miƙa mata bayanansu. Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya Kayode

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta buƙaci masu shirya zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar da su miƙa mata bayanansu.

Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja.

Kayode Egbetokun wanda ya tabbatar da cewa ’yan kasa na da cikakken ’yancin gudanar da zanga-zanga ta lumana, ya kuma shawarci masu shirya ta da su sake tunani gabanin farawa.

Egbetokun ya ce duk masu shirya zanga-zangar ko ɗaukar nauyi su miƙa wa kwamishinonin ’yan sandan jihohinsu sunayensu da adireshi domin hakan zai tabbatar da cewa an yi zanga-zangar cikin lumana.

Sauran sharuɗan da babban jami’in ’yan sandan ya gindaya sun haɗa da miƙa wa rundunar bayanan hanyoyin da za a bi yayin gudanar da zanga-zangar da kuma wurin haɗuwa da kuma tsawon lokacin da zanga-zangar za ta ɗauka.

Kazalika, Babban Sufeton ’yan sandan ya ce rahotannin sirri sun tabbatar musu an ɗauko sojojin haya daga ƙasashen ƙetare a shirye-shiryen shiga zanga-zangar.

Sai dai shugaban ’yan sandan bai yi wani ƙarin bayani kan zargin shigowar sojojin hayar ƙasashen ƙetare ba cikin zanga-zangar.

“Muna bibiyar yadda lamura ke faruwa kan zanga-zangar da take mana barazana, yayin da wasu ƙungiyoyi ke neman a yi zanga-zangar tashin hankali irin ta Kenya, wasu kuma na kira a kwantar da hankali a yi ta cikin nutsuwa ba tashin hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments