UNRWA: Fiye Da Kashi 90% Na Falastinawa A Gaza Sun Kauracewa Muhallansu

Hukumar Kula da Falasɗinawa ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta ce an tilasta wa Falasɗinawa tara daga cikin 10 barin gidajensu a

Hukumar Kula da Falasɗinawa ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta ce an tilasta wa Falasɗinawa tara daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce: “An tilasta wa Falasɗinawa 9 daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza.”

Ta ƙara da cewa “iyalai suna neman mafaka a inda za su iya samu: a makarantun da ke cike da jama’a, da gine-ginen da aka rusa, da tantuna da bola.”

Hukumar ta ce “dukkan waɗannan wurare ba su da aminci. Yanzu mutane ba su da inda za su iya tsugunawa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments