Iran Ta Yi Maraba Da ‘Sasantawar Kungiyoyin Falasdinawa’ Da Kuma Hadin Kansu

Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sasantawa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da kuma hadin kansu wanda ya faru a birnin Beijing na kasar China a

Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sasantawa tsakanin kungiyoyin Falasdinawa da kuma hadin kansu wanda ya faru a birnin Beijing na kasar China a ranar Talatan da ta gabata.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ne ya bayyana haka a cikin shafinsa na X a safiyar yau Jumma’a, ya kuma kara da  cewa, JMI zata ci gaba da tallafawa al-ummar Falasdinu har zuwa lokacinda zata sami cikekken iyncinta daga hannun yahudawan sahyoniyya. Har kuma zuwa lokacinda za’a kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci, mai babban birni a birnin Qudus mai alfarma.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya kammala da cewa hadin kan Falasdinawa zai taimaka wajen samun nasara a kan HKI, don haka ya yabawa  kasar China da wannan gagrumin aikin da ta yi na hada kan kungiyar Falasdinawa bayan tattaunawa mai zufi a tsakaninsu na kwanaki uku a birnin Beijing. Kungiyoyin falasdinawan sun sami baraka mai tsanani a tsakaninsu ne a shekara ta 2007. Bayan da aka gudanar da zabe a shekara ta 2006 sannan kungiyar Hamas ta lashe mafi yawan kujerun majalisar dokokin kasar, da kuma Isma’ila Haniya na kungiyar hamas ya zama Firai ministan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments