Hamas Ta Zargi Amurka Da Shara Karya Akan Yakin Gaza

Wani jami’i a kungiyar Hamas, Izzata al-Rashq’ ya bayyana cewa; Abinda Amurka ta bayyana na cewa ta damu akan tabarbarewar ayyukan jin kai a Gaza,

Wani jami’i a kungiyar Hamas, Izzata al-Rashq’ ya bayyana cewa; Abinda Amurka ta bayyana na cewa ta damu akan tabarbarewar ayyukan jin kai a Gaza, wata karya ce kawai domin ai da makamanta ne ake kashe mutanen Gaza.

Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr”ya ambato Izzta Rashq yana kuma cewa: Da ace Amurkan tana son ganin an kawo karshen yakin Gaza, to da ta yi hakan, domin ita ce take bai wa HKI duk wani taimako da take amfani da shi a yaki, tun daga kan makamai, siyasa, tsaro da leken asiri.

Rashq ya kuma jaddada cewa; Falasdinawa kanan yara, mata da maza sun yi shahada ne saboda amfani da makaman Amurka da ake yi a kansu.

A gefe daya jaridar “Newyork Times” ta buga wani labari da yake cewa;  Daga fara yaki zuwa yanzu Amurka ta bai wa HKI bama-bamai dubu 36, daga ciki da akwai masu sarrafa kansu 3000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments