Hizbullah Ta Kai Hari Akan  Na’urorin Leken Asirin HKI A Sansanin “Ramiya”

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kai sabon hari akan sansanin sojan mamaya na HKI na “Ramiya” wanda yake kunshe da na’urorin leken

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da kai sabon hari akan sansanin sojan mamaya na HKI na “Ramiya” wanda yake kunshe da na’urorin leken asiri da kayan yaki.

Sanarwar ta kuma ce, an yi amfani da makaman da su ka dace ne wajen kai wannan harin akan wanann sansanin, ya kuma yi barna kai tsaye.

A jiya Alhamis mai dai kungiyar ta Hizbullah ta kai wasu jerin hare-haren akan sansanonin sojojin mamaya ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuki,musamman akan sansanin manyan bindigogi na runduna ta 411 da runduna ta 288.

Wani sansanin ‘yan mamayar da harin na dakarun kungiyar Hizbullah ya shafa shi ne na “al-Ramsa”a yankin Kafar-shuba.

Tun a ranar 8 ga watan Oktoba ne dai kungiyar ta Hizbullah ta shiga cikin sahun ‘yan gwgawarmaya masu taya Falasdianwa fada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments