Wasu kafafen watsa labaru sun ambaci cewa rabin ‘yan majalisar dokokin Amurka da su ka fito daga jam’iyyar “Democrat” mai mulki a Amurka, sun kauracewa jawabin da Fira Minista Netenyahu ya yi a zauren Majalisar.
A shekarar 2015 ma dai Jumillar ‘yan majalisar da su ka kauracewa jawabin na Netenyahu sun kai 96, daga cikinsu da akwai masu wakiltar jam’iyyar “Democrat’ 58.
Rashida Talaib wacce ‘yar asalin Falasdinu ce kuma ‘yar majalisa ta halarci taron,amma tana dauke da rubutun da yake nuni da yake bayyana Netenyahu a matsayin mai aikata laifin yaki, kuma mai kisan kiyashi.