Najeriya: Sojoji Sun Ce Ba Zasu Bar Masu Zanga Zanga Su Lalata Kasar Ba

Babban helkwatan sojojin Najeriya ya bada sanarwan cewa sojojin kasar ba za su bar masu zanga zanga su lalata kasar ba. Jaridar Daily Trust ta

Babban helkwatan sojojin Najeriya ya bada sanarwan cewa sojojin kasar ba za su bar masu zanga zanga su lalata kasar ba.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto manjo janar Edward Buba daraktan watsa labarai na sojojin kasar yana fadar haka a wani taron yan jarida da yayi a yau Alhamis a Abuja.

Buba ya kara da cewa yan najeriya suna da yencin yin zanga zangar lumana, amma ba zasu bar wasu su maida zanga zangar ta cutar da wasu yan Najeriya da kuma harkokin kasuwancinsu ba.

Miliyoyin yan Najeriya dai suka kukan talaici da kuma tsadar rayuwa fiye da yadda zasu iya jurewa, tun bayan zuwan wannan gwamnatin. Don haka a cikin yan kwanakin nan, wasu sun fara kiraye kiraye a fito zanga zangar kasa gaba daya, a ranar 1 ga watan Augusta mai zuwa don nunawa gwamnatin shugaban Tinubu irin matsin lamban da suke ciki.

Manjo Buba ya kammala da cewa, wasu yan Najeriya suna ganin zanga zangar da aka yi a kasar Kenya abin koikoyo ne a garesu, amma Babu y ace zanga zangar Kenya tashin hankali ne sannan bai kai ga biyan bukata ba.

A shekara ta 2020 ma an yi zanga zanga a birnin Lagos saboda yadda wasu yansanda a lokacin suke gallazawa mutanen kasar, amma duk tare da dokar hana fita wanda gwamnatin Lagos ta lokacin ta kafa, masu zanga zanga sun ki barin unguwar Lekki a birnin na lagos, sai da sojoji suka fasa taronsu da karfi, inda wasu suke cewa an rasa rayuka da dama sanadiyyar amfani makamai wanda sojojin suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments