Adadin Falastinawa da suka yi shahada a Gaza sakamakon hare-haren Isra’ila ya 39,090

Sojojin Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa 84 a hare-haren da suka kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu ya kai 39,090 tun

Sojojin Isra’ila sun kashe wasu Falasdinawa 84 a hare-haren da suka kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu ya kai 39,090 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, in ji Ma’aikatar Lafiya a yankin.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ƙara da cewa wasu 90,147 sun jikkata a harin.

“Sojojin Isra’ila sun kashe mutum 84 tare da raunata wasu 329 a ‘kisan kiyashi’ guda takwas da aka yi wa iyalai a cikin sa’o’i 24 da suka gabata,” in ji ma’aikatar, tare da bayyana cewa an kashe 73 daga cikinsu a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Ta ƙara da cewa “har yanzu mutane da dama na maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu ɗauki.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments