Islami: Iran ta kai matsayin cin gashin kai wajen mallakar kayayyakin ayyukan nukiliya

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami  ya ce kasar ta yi nasarar kai matsayin cin gashin kai wajen samar da kayayyakin aiki

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami  ya ce kasar ta yi nasarar kai matsayin cin gashin kai wajen samar da kayayyakin aiki a masana’antar Nukiliya, yayin da a yau take sayar da kayayyakinta da da ma fasahar ayyukanta na cikin gida a kasuwannin duniya.

Mohammad Eslami ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da shafin intanet na khamenei.ir.

Ya ce, “Karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fannin fasahar nukiliya na cin gashin kansa a wannan fanni, ta yadda ayyukanmu da kayayyakinmu sun kasance abin bukata daga wasu kasashen duniya, inda ake fitar da wasunsu zuwa kasashe da dama.”

Eslmai ya kuma kara da cewa, Iran na da karfin fitar da magunguna da aka samar ta hanyar wannan fasaha zuwa kasashe daban-daban, duk kuwa da irin takunkuman da aka kakaba mata.

Masu bincike na Iran sun yi nasarar samar da tsayayyen na’urorin isotopes masu inganci.

Ya ci gaba da cewa, Iran ta samu bukatu na neman hadin kai bayan gudanar da taron kasa da kasa kan kimiyya da fasaha karo na farko tare da halartar kasashe 22 a cikin watan Mayu.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, Iran ta samu nasarori da dama a shirinta na makamashin nukiliya na lumana, tare da bijirewa takunkumin Amurka da kuma cikas da kasashen yammacin duniya suka haifar kan batun.

A matsayinta na daya daga cikin kasashe na farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, Iran tana ba da hadin kai sosai ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments