Iran: Za’a Yi Bukin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Iran A Majalisar Dokokin Kasar A Ranar Talata 30 Ga Watan Yuli

Shugaban bangaren kwamitoci da kuma al-amuran cikin gida a majalisar shoora Islami a nan kasar Iran ya bada sanarwan cewa a ranar Lahadi mai zuwa

Shugaban bangaren kwamitoci da kuma al-amuran cikin gida a majalisar shoora Islami a nan kasar Iran ya bada sanarwan cewa a ranar Lahadi mai zuwa ne za’a gudanar da bakin tabbatar da shugabancin Shugaba Mas’ud Pezeskiyan a gidan jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khamaniae a nan Tehran, majalisar ba zata gudanar da zaman da ta saba a ranar ba.

Sannan a ranar Talata 30 ga watan Yuli za’a rantsar da shugaba kasa Pezeshkiyan a cikin majalisar dokokin kasar da misalign karfe 4 na yamma.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Muhammad Salihi Jukar ya na fadar haka a yau Talata. Ya kuma kara da  cewa a zaman majalisar a yau Talata, za’a tattauna batun bukukuwan biyu ne, wato tabbatar da shugabancin Pezeskiyan da kuma karbar shaidar hakan daga jagora, da kuma batun rantsar da shi a mako mai zuwa.

Salihi ya kara da cewa majalisar ba zata gudanar da tarurrukan ta da ta saba a wadannan ranaku ba, saboda halartar wadannan bukukuwan.

A cikin watan da ya gabata ne aka zabi Dr Mas’us Pezeskiyan a matsayin shugaban kasa a zabe zagaye na biyun da aka gudanar tsakaninsa da Saedd Jalili.

Pezeshkiyan dai zai maye gurbin marigayi shugaba Ra’isi wanda ya rasu tare da wasu jami;an gwamnatinsa a cikin watan Mayun da ya gabata a wani hatsarin jirgin sama a lardin Azairbaijan ta gabas.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments