Shugaban Iran Ya Ce: Wadanda Suke Kakabawa Iran Takunkumi Sune Suke Baiwa Makiyanta Makamai Masu Guba

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Wadanda suke kakabawa Iran takunkumai a yau sune suka baiwa makiyanta makamai masu guba Zababben shugaban kasar Iran Masoud

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Wadanda suke kakabawa Iran takunkumai a yau sune suka baiwa makiyanta makamai masu guba

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Wadanda suke kakaba wa al’ummar Iran takunkumi a yau bisa dalilan wofi maras tushe, su kansu ne suka baiwa makiyan Iran makamai masu guba domin kashe al’ummar Iran a yakin shekaru takwas tsakanin Iran da Iraki.

A rubutun da ya yi a yammacin jiya Lahadi a shafinsa na dandalin sada zumunta; Shugaban na Iran ya kara da cewa: Wadanda suke kakabawa al’ummar Iran takunkumi a yau bisa dalilan marasa tushe kan zarge-zargen kera muggan makamai masu hatsari, su kansu ne suka baiwa makiya Iran muggan makamai masu guba domin share Iraniyawa daga kan doron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments