Al-Houthi : Muna Iya Tunkarar Isra’ila Fiye Da Yadda Ake Tsammani

Shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi Isra’ila cewa kasar Yemen na iya tunkarar Isra’ila fiye da yadda tsammani.  Yemen kuma ba zata

Shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen ya gargadi Isra’ila cewa kasar Yemen na iya tunkarar Isra’ila fiye da yadda tsammani.

 Yemen kuma ba zata kasawa ba wajen goyan bayan al’ummar falasdinu da ake zalinta inji shi.

Sayyed Abdul-Malik al-Houthi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jiya Lahadi, kwana guda bayan da jiragen yakin Isra’ila suka kai hare-hare ta sama kan lardin Hudaidah mai matukar muhimmanci a Yemen, a matsayin ramuwar gayya kan harin da Yemen ta kai kan Tel-Aviv ranar Juma’a.

Shugaban kungiyar Ansarullah ya ce: “Al’ummar Yemen na maraba da duk wata irin arangama kai tsaye da makiya Isra’ila, yana mai jaddada cewa Isra’ila ba za ta iya hana goyon bayan Yemen ga Gaza ba.

Al-Houthi ya kuma kara da cewa, hare-haren da Isra’ila ta kai kan Hudaidah “na nufin tattalin arzikin kasar Yemen ne,” yana mai cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka a birnin mai tashar jiragen ruwa ya tabbatar da cewa tana da nufin cutar da rayuwar Yemen din.

Shugaban kungiyar Ansurallah ya jaddada cewa, akwai bukatar a kara matsa lamba don tilastawa Isra’ila dakatar da mumunar ta’asar da take yi a zirin Gaza yayin da yakin ya shiga wata na goma.

Kalaman na baya-bayan nan sun zo ne bayan da ma’aikatar lafiya da jama’a ta Yemen ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai kan Hudaida ya kai 6.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments