Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da hare haren da jiragen yakin HKI suka kai kan yankin Zirin Gaza, kuma kan makarantar A-Falah da ake yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Naseer Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya na fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu, watanni 10 da fara yaki a gaza, sojojin yahudawan sun kashe daliban makarantu kimani 8,600 da kuma malamansu kimani 500.
Banda dakatar da karatu, an maida wadannan makaranatu mafaka ga mutane, amma duk da haka, sojojin yahudawan suna bin wadannan makarantu suna kashe mutanen da suke samun mafaka a cikinsu.
A baya bayan nan sojojin yahudawan sun kai hare hare kan makarantar Al-Falah a zirin gaza inda suka jikata Falasdinawa da dama. Daga karshen ya kammala da cewa wannan ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa, ba zai dore ba. Kuma duk wata kasa wacce ta fake da ayyukan ta’addanci don rayuwa to kuwa ba zata je ko ina ba zata rushe.