Bayanin da kungiyar ta Hamas ta fitar ya kunshi cewa; muna yin maraba da lale da bayanin da ya fito daga gwamnatin Pakistan wacce ta dauki yan sahahyoniya a matsayin masu tafka laifuka shi kuma Netenyahu a matsayin dan ta’adda.
Har ila yau, kungiyar ta Hamas ta ce, matakin da Pakistan din ta dauka wani cigaba ne gagarumi akan hanyar kare Falasdinawa daga kisan kiyashin da suke fuskanta. Haka nan kuma kungiyar ta Hamas ta kira yi dukkanin kasashen duniya da su dauki mataki na kakaba takunkumi akan ‘yan mamaya, da mayar da su saniyar ware.
Haka nan kuma kungiyar ta bukaci kasashen duniya da su rika taimakawa al’ummar Falasdinu da kayan agajin da suke bukatuwa da su, su kuma dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa.
Mai bai wa Fira ministan kasar Pakistan shawara akan harkokin siyasa, Ra’ana Sanallah ya ce; Netanyahu wani dan ta’adda ne wanda yake tafka laifuka yaki.