Kakakin Ma’aiakatar harkokin wajen Iran ya yi tir da harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa kasar Yemen, yana mai cewa; An kai wa mutanen na kasar Yemen hari ne saboda suna kare daukaka da izza da mutuncin mutanen Gaza mata da kananan da ake yi wa kisan kiyashi.
Dr. Nasir Kan’ani wanda ya kara da cewa; Harin na daren jiya ya yi sanadiyyar lallata gine-gine masu muhimmanci a tashar jiragen ruwa ta Hudaidah sannan kuma ya jikkata mutane da dama.”
Kan’ani ya kara da cewa; Abinda ya faru zai iya fadada wutar yaki a cikin wannan yakin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya dorawa HKI da masu kareta, musamman Amurka alhakin sakwanni masu hatsari da suke tattare da harin da aka kai wa kasar ta Yemen.
A daren jiya ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hari akan tashar jirgin ruwa ta Hudaidah dake kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyyar lalalta gine-gine masu muhimmanci, kamar kuma yadda wasu mutane da dama su ka yi shahada, yayin da wasu su ka jikkata.
Sojojin kasar Yemen sun sha alwashin rubanya hare-haren da suke kai wa HKI a karkashin taya mutanen Gaza yaki, kamar kuma yadda su ka ce za su dau fansa akan wannan harin na ‘yan sahayoniya.