Dakarun Yemen sun lashi takobin ci gaba da gudanar da ayyukansu na goyon bayan Falasdinawa bayan da gwamnatin Isra’ila ta kai hare-hare kan cibiyoyin fararen hula a lardin Hudeidah.
Kakakin rundunar Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana, sa’o’i bayan da jiragen yakin Isra’ila suka kai harin cewa a shirye su ke domin shiga dogon yaki da Isra’ila.
Isra’ila dai ta kai hare hare da jiragan yaki kan gine-gine, da wuraren mai, da wata tashar samar da wutar lantarki a lardin na al-Hudaidah na yammacin kasar Yemen, ranar Asabar.
Ya bayyana hare-haren da aka kai a matsayin “mummunan zalunci” wanda ya shafi gine-ginen fararen hula.
Duk da haka inji shi Sojojin Yemen, “ba za su dakatar da ayyukan da suke ba na goyan bayan Falasdinu.
Tun a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan Falasdinawa.
Sun sha alwashin ci gaba da gudanar da ayyukansu muddin gwamnatin kasar ta ci gaba da yaki da kuma kawanya wa yankin Falasdinu.
Ya kuma ce kasar Yemen ta tanadi mayar da martani ga Isra’ila kan harin da aka kai kan al-Hudaidah a ranar Asabar.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da jikkata wasu kimanin 80 a cewar rahotanni.
A wani labarin kuma Isra’ila ta sanar a yau Lahadi cewa ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harbo mata tun daga kasar Yemen.
Rundinar sojin Isra’ila ta ce makamin bai shiga kasar ba aka kakkabo shi, sakamakon karar jiniya data nuna wani abu mai hadari ya so fada wa kasar.