Martanin Kasashen Duniya Kan Hukuncin ICJ, Ga Mamayar Da Isra’ila Ke Wa Falasdinu

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da matakin kotun duniya ta ICJ ga Isra’ila na ta gaggauta dakatar da ayyukanta na

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani game da matakin kotun duniya ta ICJ ga Isra’ila na ta gaggauta dakatar da ayyukanta na mamayar yankunan Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Kudus, wanda ta kira da “haramtattu.”

Masarautar Saudiyya ta yi maraba da hukuncin yayin da ta jaddada “bukatar daukar matakai masu inganci da sahihanci don cimma daidaito da kuma cikakkiyar mafita kan lamarin Falasdinu”.

Ita ma Turkiyya ta hanyar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce al’ummar duniya “ya zama wajibi su yi tsayuwar daka wajen kawo karshen ayyukan Isra’ila”.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ta kulla huldar diflomasiyya da Isra’ila a shekarar 2020, ta “yi maraba da” hukuncin, inda Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce ta yi watsi da dukkanin matakan da suka dauka na sauya matsayin tarihi da shari’a na yankin Falasdinu da aka mamaye da kuma duk wasu ayyuka da suka saba wa kudurori kan halaccin kasa da kasa da ke yin barazana ga ci gaba da tabarbarewar zaman lafiya a yankin da kuma kawo cikas ga kokarin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A nata bangaren Afirka ta Kudu, ta ce hukuncin “ya tabbatar da cewa Pretoria, ta dade da cewa mamayar da Isra’ila ta yi wa yankin Falasdinu ya kasance haramun ne a karkashin dokokin kasa da kasa”.

Sabuwar gwamnatin Labour da aka kafa a Ingila ta ce “tana mutunta ‘yancin kai na kotun ICJ” kuma tana nazarin hukuncin kafin ta mayar da martani a hukumance.

Ita ma Aljeriya ta yi maraba da hukuncin kotun, wanda ta ce ya yi adalci ga al’ummar falasdinu, da aka dade ana zalinta.

Gwamnatin Shugaba Joe Biden, ta soki hukuncin duk da amince cewa matsugunan Isra’ila “sun sabawa” da dokokin kasa da kasa.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Mun damu matuka cewa fadin ra’ayin kotun zai dagula kokarin warware rikicin da samar da zaman lafiya mai dorewa da ake bukata cikin gaggawa tare da kasashe biyu da ke zaune kusa da juna cikin zaman lafiya da tsaro.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments