A wani lokaci yau ne babbar kotun MDD za ta bayyana ra’ayinta game da abin da doka ta ce a kan mamayar da Isra’ila ta yi wa yankunan Falasdinawa tun daga shekarar 1967, a yayin da kasashen duniya suke ci gaba da matsa lamba kan Isra’ila game da yakin da take yi a Gaza.
A gefe guda, Afirka ta Kudu ta kai karar Isra’ila a gaban kotun inda ta zarge ta da kisan kare-dangi a Gaza.
Bai zama dole a yi biyayya ga hukuncin kotun ta ICJ ba, amma matakin nata na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da fargaba kan luguden wutar da Isra’ila take yi a Gaza.
Alkalan kotun za su bayyana ra’ayinsu da misalin karfe daya na rana a agogon GMT a birnin Hague.