Rwanda : Paul Kagame, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Da Kashi 99,15%

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya lashe zaben shugabancin kasar da da kashi 99,15% na jimillar kuri’un da aka kada, abin da ya share masa hanyar

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya lashe zaben shugabancin kasar da da kashi 99,15% na jimillar kuri’un da aka kada, abin da ya share masa hanyar ci gaba da mulkin kasar nan da karin shekaru biyar masu zuwa.

Mista Kagame ya yi wa ‘yan takara biyu kacal da aka ba su damar su fafatawa da shi fintikau a zaben.

Dan takarar jam’iyyar Democratic Green Party Frank Habineza ya samu 0.53% sannan dan takarar indifenda Philippe Mpayimana ya samu 0.32%.

Jim kadan bayan ayyana nasarar ta wucin-gadi, wacce ta ba wa Kagame damar wa’adi na hudu, ya godewa ‘yan Rwanda a cikin wani jawabi da ya gabatar a ofishin jam’iyyarsa ta Rwandan Patriotic Front (RPF).

Sai a ranar 20 ga watan Yuli ne cikakken sakamakon wucin-gadi zai fito, sannan ainihin sakamakon zaben zai fito ranar 27 ga Yuli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments