Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta nada Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye a matsayin mai shiga tsakani na musamman domin tattaunawa da kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da suka balle daga kungiyar.
ECOWAS, na son kasashen kungiyar Sahel Alliance AES sun sauya tunani game shirin nasu na ficewa daga kungiyar,” kamar yadda ECOWAS ta bayyana a sanarwar bayan babban taronta na Abuja, babban birnin Najeriya ranar Lahadi.
Shugaban na Senegal zai jagoranci tawagar tattaunawar tare da hadin gwiwar takwarsansa na Togo, Faure Gnassingbe,inji sanarwar ta Ecowas.
Mista Faye na halartar taron na ECOWAS ne a karon farko tun bayan zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasar ta Yammacin Afirka a watan Maris.
Shugabannin kungiyar sun yi taron ne ranar Lahadi bayan kasashen uku da sojoji ke mulki, wato Nijar da Mali da Burkina Faso sun sanya hannu kan wata yarjejeniya ta kafa wata hadaka da suka kira kungiyar Sahel of Alliance States ko kuma AES a takaice.
Sun balle ne daga kungiyar ta Yammacin Afirka a watan Janairu bayan kuniyar ta dauki tsauraran matakai kan juyin mulkin da aka yi a kasashen.