Shugabannin Mulkin Soji Na Kungiyar AES Na Taro A Nijar

Shugabannin mulkin sojin Kungiyar hadakar kasashen nan uku na Sahel da ake kira (AES), a takaice, na gudanar da taronsu irinsa na farko a birnin

Shugabannin mulkin sojin Kungiyar hadakar kasashen nan uku na Sahel da ake kira (AES), a takaice, na gudanar da taronsu irinsa na farko a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Taron ya hada da Kanal Asimi Goita na Mali, da Kyatin Ibrahim Traore na Burkina faso da kuma Abdurahmane Tiani na Nijar.

Kafin nan bakin dake halartar taron sun samu kyakyawan tarbe daga dimbin al’ummar Yamai a jiya Juma’a.

Taron kasashen uku da dukkansu suka fice daga kungiyar ECOWAS, na zuwa ne gababin wani taron kungiyar ta Ecowas a ranar Lahadi.

A ranar 28 ga watan Janairun 2024, ne kasashen Burkina faso, Mali da kuma Nijar, suka fitar da sanarwa bi da bi domin bayyana matakin raba gari da kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO.

Kasashen na masu zargin kungiyar ta ECOWAS, da rashin adalci, da kaucewa muhimman maradun kafa ta, hasali ma da zama ‘yar amshin shatan shatan kasashen yammacin duniya domin cin amanar kasashe mambobinta da kuma kasawa wajen dafawa yakar ayyukan ta’addanci da ya addabi yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments