Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul-Islam Muhammad Jawad Hajj Ali Akbari ya bayyana cewa: Shika-shikan gudanar da mulki a Musulunci sun dogara ne kai tsaye ko kuma a fakaice kan kuri’un jama’a, kuma hakan yana gudana ne da kuri’un jama’a ta hanyar tsarin zabe.
Limamin ya fayyace cewa: Wajibi ne muminai su gudanar da mu’amala a karkashin ka’idojin aminci da zaman lafiya da sauran mutane bisa ka’idojin zamantakewa na addini. Wanda hakan na nufin kada a cutar da kowa kuma a kiyaye mutunci mutane.
Hujjatul Islam Haj Ali Akbari ya kara da cewa: A yayin gudanar da zabuka, da yake daya daga cikin muhimman abubuwan da suke nauyin al’umma, wani nauyi ne da ya rataya a wuyar musulmi a tsakanin al’umma, kuma wasu al’amuran sun shafi rayuwar al’umma gaba daya. Sannan kuma al’amura ne da suka shafi asali da kuma jigon rayuwar al’ummar musulmi, kamar yadda a cikin adabin alkur’ani mai girma ake kiran wadannan al’amura da al’amari da ya hada dukkan komai da komai. Limamin sallar juma’ar birnin na Tehran ya fayyace cewa: Idan aka zo batun rayuwa da daukaka da kimar al’ummar musulmi da kuma gina ginshikin karfi a tsarin Musulunci, wannan lamari yana daga ciki, kuma dukkanin al’umma suna da hakkin da ya rataya a wuyansu sannan dole ne ya kasance su taka rawar gani a wannan fage.