Kwamandan Sojin Sama Na Iran Ya Jaddada Muhimmacin Zaben Iran

Kwamandan rundunar sojin sama ta dakarun kare juyin juaya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Fitowar mutane a zaben shugaban kasa zagaye na biyu

Kwamandan rundunar sojin sama ta dakarun kare juyin juaya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Fitowar mutane a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Iran zai kara karfi da martabar kasar

Kwamandan sojojin sama na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Hajizadeh ya bayyana cewa: Fitowar al’ummar Iran a zabukan, zai taimaka wajen karfafa karfi da kuma matsayin Iran a yankin da ma duniya baki daya.

A ganawar da ya yi da manema labarai a yau Juma’a, a lokacin da yake kada kuri’a a masallacin Abu Zarr da ke birnin Tehran, Haji Zadeh ya yi furuci da cewa; Fitowar al’ummar Iran zuwa zabe, wajibi ne na shari’a kuma hidima ce ga kasa, don haka ya zama dole al’umma su gaggauta fitowa domin zaben wanda ya fi cancanta ya shugabance su.

Ya kara da cewa: Al’ummar Iran sun sadaukar da shahidai sama da dubu dari da saba’in don kare kasarsu, don kada su yi hasarar ko da tako daya na kasarsu ga wasu masu son mamaye musu kasa. Don haka ya bayyana fatansa na ganin an zabi mutum nagari a matsayin sabon shugaban kasa na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Ya ci gaba da jaddada cewa: Wajibi ne al’ummar Iran su kiyaye hadin kan su da kuma shiga cikin zabuka, kuma wannan fitowa zabukan ya zama wajibi ga kasar, kuma kowace kuri’a da za a kada tana matsayin makami mai linzami ne kan makiya tsarin Musulunci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments