Majalisar Dinkin Duniya ta bada umurnin janyewar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka mamaye kashi daya cikin uku na Zirin Gaza lamarin da ya hana kokarin raba kayan agaji
Wani babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Umarnin janyewar sojojin gwamnatin Isra’ila daga yankunan da suka mamaye na Zirin Gaza da ya kai kashi daya cikin uku tare da hana yunkurin kungiyoyin kasa da kasa na inganta harkokin isar da kayan agaji ta hanyar mashigar Kerem Shalom, lamari mai muhimmanci domin rage mummunan halin da al’umma suka shiga.
Gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta soki ayyukan hukumomin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya da suke jagorantar kokarin shigar da kayan agaji zuwa yankin Gaza mai dauke da mutane da suka kai miliyan 2.3.
A wannan watan ne dai sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar da shirinsu na dakatar da kai hare-hare kan Falasdinawa da rana kadai, domin saukaka Shirin isar da kayan agaji ga al’ummar Gaza daga mashigin Kerem Shalom, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce tashe-tashen hankula sun Sanya har yanzu lamarin na da matukar hadari, kuma ta daura alhakin maido da zaman lafiya da tsaro a Gaza a wuyar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.