Al’Houthi : Katafaren Jirgin Ruwan Yakin Amurka Bai Kai Kimar Da Aka Bashi Ba

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya yabawa sojojin ruwa na kasar dangane da ayyukan da suke aiwatarwa a tekun Red

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya yabawa sojojin ruwa na kasar dangane da ayyukan da suke aiwatarwa a tekun Red Sea don hana dukkan jiragen ruwa wadanda suke da dangantaka da HKI ko wadanda suke tare da ita waucewa ta tekun.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana  fadar haka a jawabin makon makon da ya saba gudarnawa a ranakun Alhamis.

Ya kuma kara da cewa yakin da ke gudana tsakanin Yemen da kuma Amurka da kawayenta, ya tabbatar da cewa, kataparen jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki na kasar Amurka wanda ake kira ‘Kariya ‘ bai kai kimar da ake bashi ba, bai kuma cancanci kudaden da ake kashe masa ba, musamman bayan da sojojin ruwa na kasar Yemen suka boge shi da makamai masu linzamin da suka kera a kasar ta Yemen.

Labarin ya kara da cewa, wasu jami’an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa hare haren kasar Yemen suna da karfi kuma sun bayyana raunin makaman kasar Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments