Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun kai gagarumin hare hare kan waurare da dama a kan HKI bayan da ta kashe daya daga cikin kwamandojojin kungiyar a kudancin kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare a kuidancin kasar Lebanon a jiya Alhamis, inda suka kai Muhammad Ni’mah Naseer kwamandan rundunar ‘Aziz’ ta kungiyar ta Hizbullah da wasu wadanda suke tare da shi ga shahada.
Labarin ya kara da cewa kungiyar ta yi amfani da makaman roka samfurin Burkan da Falaq na zamani, da kuma wasu nau’in makaman, inda suka cillasu kan barikokin sojojin HKI guda 5 da wata kasuwa wato “Mall” da a garin Acre na tuddan Golan na kasar Siriya da HKI ta mamaye.
Majiyar HKI ta bayyana cewa soja guda ya rasa ransa sannan wasu da dama sun ji munanan raunuka.
Kamfanin dillancin Labaran ‘Yedi’oth Ahronoth ya bayyana cewa tawagar kwana kwana har guda 25 ne gwamnatin HKI ta aika don kashe gobarar da hare haren dakarun Hizbullah suka haddasa a wurar 10 a yankin Tuddan Golan. Da yankin Galilee ta sama.
Labarin ya kamala da cewa hare haren HKI sun kai kwamnadan rundunar Aziz Mohammed Nimah Nasser , da wadanda suke tare da shi ga shahada ne a kusa da garin Tyre na kudancin kasar Lebanon. Nasser dais hi ne babban kwamandan dakarun Hizbullah mafi girma da kai ga shahada tun fara yakin tufanul aksa watanni kimani 9 da suka gabata.