Kasashen Larabawa Sun Bukaci A Kori HKI Daga Babban Zauren  MDD

Kungiyar kasashen larabawa ta bukaci tawagar kasashen a babban zauren MDD ta fara aiki don ganin an dakatar da HKI daga halattar tarurrukan majalisar. Kamfanin

Kungiyar kasashen larabawa ta bukaci tawagar kasashen a babban zauren MDD ta fara aiki don ganin an dakatar da HKI daga halattar tarurrukan majalisar. Kamfanin dillancin labaran WAFA ta Falasdinawa ta bayyana cewa kungiyar ta gabatar da wannan bukatar ce a wani taron gaggawan da ta gudanar a birnin Alkahira a jiya Alhamis.

WAFA ya  kara da cewa, wakilan kasashen na Larabawa sun ce dole ne a kori wakilin HKI daga babban zauren majalisar, saboda sabawa dokokin majalisar da take yi, dokoki wadanda suka shafi yaki a gaza. Musamman na tsagaita wuta, da wadanda suka shafi hakkin bil’adama. Jakadan kasar Falasdinu a majalisar ya yi maraba da wannan matakin da kungiyar kasashen larabawna ta dauka, ya kuma kara da cewa: wakilan kungiyar a matakin jakadunsu na din din din a MDD sun kuduri anniyar fara shirin korar HKI daga Majalisar.

Saboda rashin mutunta dokokinta, da kuma zama kasa wacce take mulkin mallaka a kasar Falasdinu da ta mamaye, banda haka HKI ta kuma zama barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya. Har’ila yau ta yi burus da dukkan dokokin MDD da kuma kudurorin kasa da kasa.

Jakadan ya kara da cewa, irin wannan matakin ne ya kawo karshen tsarin wariyar launin fata a kasar Afirka ta kudu a shekarun da su gabata. Ya ce a ranar 19 ga watan Decemban shekara 1974 babban zauren MDD ya bada shawarar dakatar da kasar Afirka ta gudu daga halattar tarurrukan babban zauren saboda tsarin wariyar launin fatan da take aiwatarwa a kasar Afirka ta kudu.  Sannan a shekarar ne shugaban babban zauren MDD karkashin jagorancin kasar Algeria ya ki karban takardun gwamnatin wariya ta kasar Afirka ta kudu, da haka kuma aka kama hanyar faduwar gwamnatin waria a kasar Afirka ta kudu wanda ya tabbata a shekara 1990’s

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments