Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare cikin dare a Gaza duk da rahotannin yunkurin sake farfado da tattaunawar tsagaita wuta.
Rahotanni sun ce jiragen saman Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a zirin Gaza cikin dare a daidai lokacin da aka bayyana shirin sake farfado da tattaunawar kawo karshen yakin da Isra’ila ke yi a yankin Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu Wafa ya bayar da rahoton cewa, an kashe mutane biyar da suka hada da kananan yara uku a wani harin bam da Isra’ila ta kai a yankin Jabalia al-Balad da ke arewacin Gaza.
Ita kungiyar agaji Red Crescent ta Falasdinu ta ce, an kashe mutum daya tare da jikkata uku a wani harin da jiragen saman Isra’ila suka kai kan titin as-Sikka, da ke gabashin sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia, wanda kuma ke arewacin Gaza.
Wasu rahotannin sun ce Isra’ila ta kai hare-hare da makaman roka a garin al-Nasr da ke arewa maso gabashin birnin Rafah, yayin da motocin yaki masu sulke suka shiga yankin.
Wannan na zune a daidai lokacin da rahotanni suka bayyana cewa an samu ci gaba a tattaunawar da aka yi tsakanin Hamas da Isra’ila domin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sako ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su.
Isra’ila ta aike da wata tawaga karkashin jagorancin babban jami’in hukumar leken asirin kasar ta Mossad, David Barnea zuwa Qatar domin tattaunawar.