Australia : Sanata Fatima, Ta Fice Daga Jam’iyya Mai Mulki, Saboda Goyan Bayan Falasdinu

Sanata Fatima Payman, yar siyasar da ta fara saka hijabi a Australia, ta fita daga jam’iyya mai mulki ta Labor a kasar kwanaki kadan bayan

Sanata Fatima Payman, yar siyasar da ta fara saka hijabi a Australia, ta fita daga jam’iyya mai mulki ta Labor a kasar kwanaki kadan bayan ta nuna kin jinin kudirin jam’iyyar na adawa da kafa kasar Falasdinawa.

Matashiyar mai shekaru 29, ta kasance musulma wadda iyalinta suka tsere daga Afghanistan bayan Taliban ta kwace mulki a 1996.

Yayin taron manema labarai kan matakin da ta dauka, Sanata Fatima Payman, ta bayyana cewa “ba kamar abokan aikina ba, na san yadda ake ji ace kai kadai ne kake fafutuka kan rashin adalci.

Ba zan iya yin shiru ba kan munanawa mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Batun dai Gaza ya zamo batun siyasa mai zafi a Australia da kowanne bangare ke taka tsantsan akansa.

A makon da ya gabata, Fatima Payman ta bijirewa jam’iyyarta ta Labour inda ta goyi bayan jam’iyyar The Greens kan kudirin neman majalisar dattawa ta amince da kasar Falasdinu.

Daga nan sai Firaministan kasar Anthony Albanese ya dakatar da ita a ranar Lahadi.

Payman, ta ce za ta ci gaba da rike mukaminta na yammacin Australia a matsayin mai cin gashin kanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments