Iran : ‘Yan Takaran Zaben Shugaban Kasa Na Muhawara Ta Biyu A Gidan Talabijin

‘Yan takara biyu da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun fara tafka muhawara ta biyu da ake watsawa kai

‘Yan takara biyu da ke neman kujerar shugabancin kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili, sun fara tafka muhawara ta biyu da ake watsawa kai tsaye a gidan talabijin din kasar gabanin zaben da za;a gudanar a ranar Juma’a.

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin muhawara guda biyu gabanin zaben na ranar 5 ga watan Yuli, wanda ya shafi batutuwan tattalin arziki.

A yammacin ranar Litinin ne aka gudanar da muhawara ta farko kan batutuwan siyasa da al’adu.

A ranar Lahadi ne aka fara yakin neman zaben zagaye na biyu a hukumance, kwana guda bayan sanar da sakamakon zaben ranar 28 ga watan Yuni da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar.

Pezeshkian da Jalili ne suka samu mafi yawan kuri’u amma babu wani dan takara da ya iya samun cikakken rinjaye, wanda ya sanya za’a je zagaye na biyu.

Pezeshkian tsohon ministan lafiya kuma babban dan majalisa daga birnin Tabriz da ke arewa maso yammacin kasar, na fafatawa da Jalili wanda tsohon mai jagorantar shawarwarin nukiliyar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments