Kungiyar hadin kan Larabawa ta janye daga matsayinta na sanya kungiyar Hizbullah a matsayin “kungiyar ta’addanci”, Hossam Zaki, mataimakin sakatare-janar na kungiyar Larabawa ya sanar da hakan.
Zaki ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka watsa ta tashar talabijin ta Al-Qahera ta Masar cewa, “A cikin hukunce-hukuncen kasashen Larabawa da suka gabata, an sanya kungiyar Hizbullah a matsayin kungiyar ta’addanci.
A cewar babban jami’in, “kasashen mambobin kungiyar sun amince cewa, a janye kungiyar Hizbullah daga cikin kungiyoyi da ake kira na ta’addanci.
A nata bangaren, jaridar Al-Akhbar ta kasar Labanon ta nakalto majiyoyi na cewa, Zaki ya sanar da kungiyar Hizbullah cewa kungiyar Hadin kan kasashen Larabawa ta yanke shawarar janye matakin da ta dauka a baya kan Hizbullah da ke danganta kungiyar da ayyukan ta’addanci, kuma ta yi imanin cewa, Hizbullah tana da muhimmiyar rawa a makomar kasar Lebanon.