A ganawarsa da wakilan taron shahidai ‘yan gwagwarmaya da masu kare wurare masu alfarma na kasa da kasa a jiya Asabar: Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Kare wuraren ibada masu alfarma wani lamari ne mai girma da muhimmanci, kuma daya ne daga cikin abubuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kebanta da shi a duniya, yana mai jaddada cewa: Kasantuwar matasa daga al’ummomi daban-daban da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare wurare masu alfarma lamari ne da ke nuni da cewa. Juyin juya halin Musulunci yana da karfin sake haifar da kishi da zaburar da zukatan al’umma zuwa ga ruhin juyin juya halin Musulunci na farko tun bayan fiye da shekaru arba’in da suka gabata.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kuma yaba da tunawa da dukkanin shahidan da suke kare wurare masu alfarma da kuma bangarorin gwagwarmaya, musamman kwamanda shahidi Qasim Suleimani, yana mai fayyace cewa: Kare wuraren masu alfarma wani bangare ne na kare tunani da burin ma’abuta wadannan hubbaren musamman Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s}, ya kara da cewa: Manufofin Jagororin Shiriya na Iyalan Gidan Manzon Allah tsarkaka {a.S} kamar wanzar da adalci, ‘yanci, gwagwarmaya domin kare gaskiya da kuma sadaukarwa a kan hanyar gaskiya, sune abubuwan bukatu a ko da yaushe wurin masu dauke da rayayyun zukata.