Bagheri Kani: Dangantaka Tsakanin da Saudiyya Na Ci Gaba Da Kara Bunkasa

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya bayyana yadda alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiya take

Ministan harkokin wajen kasar Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya bayyana yadda alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiya take ci gaba da kara bunkasa a dukkanin bangarori, yana mai jaddada cewa Tehran da Riyadh sun kudiri aniyar ci gaba da yin aiki tare a fagage da dama domin ci gaban al’ummominsu.

A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan Al Saud a daren jiya,  Bagheri Kani ya mika godiyarsa ga mahukuntan Saudiyya kan samar da wadatattun kayayyakin bukatuwa na alhazai da suka fito daga kasar Iran, da kuma yadda suka nuna kulawa matuka.

Mataimakin Ministan harkokin wajen Saudiyya Waleed al-Khereiji ya yaba da ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Iran rikon kwarya a birnin Tehran a gefen taron ministocin kungiyar hadin gwiwar kasashen Asiya karo na 19, yana mai bayyana huldar diflomasiyya ke tsakanin kasashen biyu a matsayin mai matukar alfanu ga kasashen biyu da kuma duniyar musulmi.”

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kuma yi karin haske kan irin ta’asar da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya da kuma yammacin gabar kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

” Barazanar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa kasar Labanon ya yi daidai da laifukan yakin da take aikatawa kan al’ummar Gaza.

Bagheri Kani ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na kokarin cike gurbin shan kayen da take yi ne a Gaza ta hanyar fadada fagen yaki da laifuka zuwa wasu yankuna, domin kuwa har yanzu ta kasa cimma ko daya daga cikin manufofin yakin da ta shelanta kan a lummar yankin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments