Isra’ila Na Ci Gaba Da Yin Ta’annuti A Yankin Rafah Da Ke Gaza

Sojojin Isra’ila sun sake kutsawa cikin yankuna biyu na arewaci da kudancin Gaza, kuma jami’an kiwon lafiyar Falasdinu sun ce harin tankokin yaki a Rafah

Sojojin Isra’ila sun sake kutsawa cikin yankuna biyu na arewaci da kudancin Gaza, kuma jami’an kiwon lafiyar Falasdinu sun ce harin tankokin yaki a Rafah ya kashe akalla mutum 11.

Mazauna yankin da kafafen yada labarai na cikin gida sun ce tankokin yaki sun kara yin yamma zuwa unguwar Shakoush da ke Rafah, lamarin da ya tilasta wa dubban mutanen da suka rasa matsugunansu barin sansaninsu, suka nufi arewa zuwa Khan Younis da ke kusa.

Wani mazaunin yankin, wanda ya yi magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ce wasu manyan katafiloli a yankin Shakoush na tara yashi domin tankunan yaƙin Isra’ila su samu tsayawa a baya.

Ya ƙara da cewa, “Wasu iyalai suna zaune a yankin da aka kai farmakin, kuma a yanzu dakarun mamaya sun yi wa wajen ƙawanya.

“Halin da ake ciki yana da matukar hadari kuma iyalai da yawa suna tafiya zuwa Khan Younis, har ma daga yankin Mawasi, saboda al’amura sun kasance marasa aminci a gare su,” in ji mutumin, wanda ya koma arewa cikin dare.

A gefe guda kuma, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai sabon farmaki a unguwar Shujaiya da ke arewacin Gaza, inda tankokin yaƙi suka kutsa wajen a ranar Alhamis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments