Sojojin Yemen sun kai hari kan jirgin ruwa “Waler” a wani farmakin hadin gwiwa da dakarun kasar Iraki
A wata sanarwa da sojojin kasar Yemen suka fitar, a jiya Juma’a, sun bayyana kaddamar da wani harin hadin gwiwa tare da ‘yan gwagwarmayar kasar Iraki, inda suka yi barin wuta kan jirgin ruwan “Waler” ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.
Sanarwar ta bayyana cewa: A bisa matakin taimakawa al’ummar Falastinu da ake zalunta musamman a ZirinGaza, ‘yan gwagwarmaya sun mayar da martani ga kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan al’ummar Falastinu a Zirin Gaza.
Sojojin Yemen da hadin gwiwar ‘yan gwagwarmayar Iraki sun gudanar da ayyukan soji masu inganci da muhimmanci kan makiya da suka hada da kai harin kan jirgin ruwan Waler da ke tafiya a tekun Mediterrenea dauke mai fetur zuwa tashar jiragen ruwan Haifa na haramtacciyar kasar Isra’ila da jiragen sama marassa matuka ciki, saboda sabawa matakin hana shiga cikin tasoshin jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye.