An Yi Yunkurin Juyin Mulki A Kasar Boliviya Da Bai Yi Nasara Ba Tare Da Kama Madugun

‘Yan sandan Boliviya sun kama jagoran juyin mulkin kasar, yayin da shugaban Boliviya ya yaba da goyon bayan jama’a gare shi ‘Yan sandan kasar Boliviya

‘Yan sandan Boliviya sun kama jagoran juyin mulkin kasar, yayin da shugaban Boliviya ya yaba da goyon bayan jama’a gare shi

‘Yan sandan kasar Boliviya sun kama wani tsohon janar din kasar da ya yi yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar, inda shugaban kasar Luis Arce ya tabbatar da ikonsa a kan sojojin kasar tare da godewa al’umma kan ci gaba da goyon bayan gwamnatinsa.

Dakarun Juan Jose Zuniga, wanda aka kora a farkon makon nan a matsayin kwamandan rundunar sojojin Boliviya shi da tawagarsa sun kai farmaki fadar shugaban kasa da ke La Paz babban birnin kasar a yammacin jiya Laraba, inda suka mamaye dandalin da ke wajen fadar shugaban kasar, da wasu muhimman gine-ginen gwamnati. Kafafen yada labarai sun ce wata tankar yaki ce ta toshe kofar shiga fadar shugaban kasar.

Sai dai Zuniga ya bukaci sojojin a cikin sa’o’i kadan da su janye, bayan da shugabannin kasashen duniya suka yi Allah wadai da matakin da sojojin suka dauka a matsayin haramtacce.

Janyewar sojojin ya biyo bayan kama Zuniga bayan da babban lauyan gwamnatin kasar ya bude bincike kan mamaye fadar shugaban kasar.

Ministan gwamnatin Boliviya Eduardo del Castillo ya ce baya ga kame Zuniga, an kuma tsare tsohon mataimakin kwamandan rundunar sojin ruwan kasar Juan Arnez Salvador.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments