Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Allah Wadai Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar Boliviya

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Boliviya Jamhuriyar Musuluncita Iran ta yi

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Boliviya

Jamhuriyar Musuluncita Iran ta yi Allah-wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Boliviya, tana mai jaddada bukatar maido da doka da oda a kasar da ke Kudancin Amurka.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Naser Kan’ani ya bayyana a yau Alhamis cewa: Jamhuriyar Musuluncita Iran tana yin Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi kan tushen dimokaradiyya da kuma harin da aka kai kan cibiyoyin dimokaradiyya da halattacciyar gwamnatin Boliviya.

Sannan Iran ta jaddada mahimmancin maido da doka da oda da kuma maido da mulki ga halattcciyar gwamnatin Boliviya da take bisa tsarin doka.

Dakarun Juan Jose Zuniga, wanda aka kora a farkon makon nan a matsayin kwamandan sojojin Boliviya, sun kai farmaki fadar shugaban kasa da ke La Paz babban birnin kasar a yammacin jiya Laraba, inda suka mamaye dandalin da ke wajen fadar shugaban kasar, da wasu muhimman gine-ginen gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments