Kasar Pakistan Ta Yaba Wa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran A Fagen Goya Mata Baya A Yaki Da Ta’addanci

Ministan Tsaron Pakistan ya bayyana cewa: Iran ce take goyon bayan kasarsa wajen fuskantar ta’addanci Ministan tsaron kasar Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya bayyana cewa:

Ministan Tsaron Pakistan ya bayyana cewa: Iran ce take goyon bayan kasarsa wajen fuskantar ta’addanci

Ministan tsaron kasar Pakistan Khawaja Muhammad Asif ya bayyana cewa: Kasarsa ta kuduri aniyar kawar da tushen ta’addanci a kan iyakokinta na kudu maso yammacin kasar kuma tana samun goyon baya da tallafi daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wannan fanni.

A wata hira da ya yi da kafar yada labaran Pakistan a yau Alhamis, Asif ya bayyana takaicinsa kan yadda matsalar ta’addanci ta janyo gibi a kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, yana mai cewa Pakistan ba ta samun ingantaccen hadin kai daga makwabciyarta ta yamma   .

Haka nan kuma ya yi ishara da hadin gwiwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take baiwa Pakistan wajen tunkarar ta’addanci inda ya ce babu wani kalubale da Iran ke fuskanta dangane da hakan, yana mai jaddada cewa kasarsa na samun goyon bayan Iran a fagen kawar da ta’addanci.

Ya kara da cewa: Sabon farmakin sojojin da ake gudanarwa a karkashin taken “Karfin Azama”, ya mayar da hankali ne musamman wajen zakulo wadanda ke dagula harkokin tsaro da masu shirya kai hare-haren ta’addanci, kuma aikin ya kai har zuwa lardunan Khyber Pakhtunkhwa da Balochistan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments