Gwamnatin Kasar Canada Ta Haramta Zaben Shugaban Kasan Iran A Kasar

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran ya bada sanarwan ceba Iraniwa mazauna kasashen Canada da Saudia ba zasu kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran ya bada sanarwan ceba Iraniwa mazauna kasashen Canada da Saudia ba zasu kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a gobe jumm’a ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ahmad Vahidi yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa a kasar Canada gwamnatin kasar ta hana dubban Iraniyawa ma zauna kasar kada kuri’unsu a duk wani cibiyar zaben da za’a samar a kasar.

A kasar Saudiya kuma gwamnatin kasar bata bada amsa ga bukatar gwamnatin kasar na samar da cibiyoyin zabe a kasar don dubban Iraniyawa mahajjata da suke kasar har yanzu ba.

Wahidi ya kara da  cewa akwai cibiyoyin kada kuria har guda 300 a kasashen duniya daban daban, inda iraniyawa ma zauna kasashen waje suke iya kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa karo na 14 a kasarsu.

A cikin gida kuma ministan ya cewa akwai lardunan zabe har guda 60,000 a kasar, rumfunan zabe 90,000 a cikinsu. Sannan mutane kimani miliyon 61 ne suka cancanci kada kuri’a a zaben na gobe jumma’a 28 ga watan Yuni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments