Mokhber : Yarjejeniyar Iskar Gas Ta Tsakanin Iran Da Rasha Za Ta Amfani Yankin

Shugaban riko na kasar Iran Mohammad Mokhber ya ce yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tun da farko tsakanin kasar da Rasha kan yiwuwar shigo

Shugaban riko na kasar Iran Mohammad Mokhber ya ce yarjejeniyar fahimtar juna da aka kulla tun da farko tsakanin kasar da Rasha kan yiwuwar shigo da iskar gas na Rasha zuwa Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata amfani muradun daukacin yankin.

Mohammad Mokhber ya bayyana hakan ne, yayin da yake zantawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho jiya Laraba.

Mokhber ya ce “[yiwuwar] aiwatar da shirin mika iskar gas na Rasha zuwa Iran ba wai zai amfani tattalin arzikin kasashen biyu ba kawai, a’a har ma da muradun yankin baki daya.”

Jiya Laraba ne aka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ministan mai na Iran Javad Owji da manzon musamman na Tarayyar Rasha kuma shugaban kamfanin makamashi na Gazprom na Rasha Alexey Miller.

Idan yarjejeniyar ta tabbata, hakan zai  baiwa Iran damar shigar da iskar gas daga Rasha da kuma shigar da shi kasashen Iraki, Turkiyya da Pakistan.

Mokhber bayyana yarjejeniyar a matsayin wani babban mataki na zurfafa dangantakar dake tsakanin Rasha da Iran.

A nasa bangaren, Shugaba Putin ya bayyana jin dadinsa game da rattaba hannu kan yarjejeniyar ta fahimtar juna, yana mai tabbatar da cewa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ba zai tsaya kan takarda ba, zai kai ga matakin aiwatarwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments