Iran Ta Yi Tir Da Harin Ta’addancin Da Ya Yi Ajalin Sojoji A Nijar

Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da ya yi ajalin sojoji da raunata wasu a Jamhuriyar Nijar. Da yake sanar da kakakin ma’aikatar harkokin

Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da ya yi ajalin sojoji da raunata wasu a Jamhuriyar Nijar.

Da yake sanar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanani, ya yi tir da harin, da ya yi sanadin rayuwar sojoji da kuma farar hula da raunata wasu a Nijar.

Mista Kanani, ya bayyana alhininsa da na kasarta Iran, game da hasarar rayukan da aka samu sanadin harin na ta’addanci a jihar Tillabery.

Ya kuma nuna goyan baya ga gwamnatin kasar ta Nijar da kuma al’ummarta musamman iyalai da dangin wadanda lamarin ya shafa.

Ya kuma ce Iran, har kullum tana mai adawa da duk wani salon a ayyukan ta’addanci dake barazana ga rayuwar bil adama dama kasa da kasa, ya kuma jadadda bukatar hada karfi da karfe na duk sassan duniya domin ganin bayan wannan barazana.

Wata Sanarwa da ma’aikatar tsaron Nijartda aka karanta a gidan talabijin din kasar ta ce Hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan ta’adda” sun kai wa jami’an tsaro hari a kusa da kauyen Tassia, na yankin Tillaberi da ke iyaka da Mali da Burkina inda suka kashe sojoji 20 da jikkata wasu 9.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments