MDD: Hare-Haren Isra’ila Suna Nakasa Akalla Yara Goma A Kowace A Zirin Gaza

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kakkausar suka game da rikicin Gaza da yaki ya daidaita, suna masu cewa yara 10 a rana suna rasa

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kakkausar suka game da rikicin Gaza da yaki ya daidaita, suna masu cewa yara 10 a rana suna rasa kafa daya ko biyu sannan Falasdinawa rabin miliyan na fama da matsananciyar yunwa.

Isra’ila na ci gaba da ta’azzara hare-haren da take kai wa Gaza da kuma hare-hare kan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas sakamakon harin na ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da ta ci gaba da killace yankin na mutane miliyan 2.4.

Jami’an Falasdinawa sun ce wani harin ya kashe mutum 10 ‘yan gidan shugaban siyasar Hamas Ismail Haniyeh ciki har da ‘yar’uwarsa.

Sojojin Isra’ila ba su tabbatar da kai harin ba, wanda hukumar kare fararen hula a Gaza ta ce an kai harin ne a gidan ‘yan’uwan shugaban da ke arewacin sansanin ‘yan gudun hijira na Al Shati, inda ɓaraguzan gini ya danne wasu gawarwakin.

A nata bangaren kungiyar global hunger monitor, ta bayar da wani rahoto da ke cewa,  Ana ci gaba da fuskantar yiwuwar faɗawa cikin bala’in yunwa a dukkan yankunan Gaza a yayin da Isra’ila take ci gaba da kai hare-hare a yankin sannan ta taƙaita agajin da ake shigarwa.

Fiye da mutum 495,000, wato sama da kashi ɗaya cikin biyar na al’ummar yankin Gaza na fuskantar masifar yunwa da rashin abinci, in ji ƙungiyar.

Ta ƙara da cewa da alama abincin da aka kai arewacin Gaza a watan Maris da Afrilu ya rage fuskantar yunwa a wasu yankuna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments