Adadin Faastinawa Da Suka Yi Shahada a Hare-haren Isra’ila a Gaza Ya Kai 37,626

A rana ta 263 da Isra’ila ta kwashe tana aiwatar da kisan kare dangi a Gaza, adadin falastinawa da suka yi shahada ya kai 37,626

A rana ta 263 da Isra’ila ta kwashe tana aiwatar da kisan kare dangi a Gaza, adadin falastinawa da suka yi shahada ya kai 37,626 galibinsu jarirai, mata da yara, sannan kuma ta jikkata sama da mutum 86,098, kuma mutum sama da 10,000 suna karkashin baraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500.

Sojojin yahudawan Isra’ila sun yi luguden wuta a sassa da dama a faɗin yankin Gaza, sannan mazauna Rafah sun bayar da rahoton yin gumurzu a yankin na kudancin Falasɗinu.

Ganau sun ce yaƙi ya yi ƙamari a yankin Tel Al Sultan na yammacin Rafah, inda tankokin yaƙi suka riƙa ƙoƙarin kutsawa arewaci ana tsaka da ba-ta-kashi. Mayaƙan Hamas da Islamic Jihad sun ce sun yi amfani da rokoki da bama-bamai wajen kai hari kan dakarun Isra’ila.

Tun a watan Mayu, Isra’ila ta mayar da hankali wurin kai hari ta ƙasa a Rafah, da ke kan iyakar Gaza da Masar, inda kusan rabin mutane miliyan 2.3 na Gaza suke samun mafaka bayan sun tsere daga arewaci. Tuni dai mutane suka riƙa tserewa daga yankin.

Ma’aikatan lafiya sun ce Isra’ila ta kashe Falasɗinawa biyu a harin da ta kai da makami mai linzami a Rafah ranar Laraba da safe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments