Daraktan sashen kula da ayyukan lafiya na gaggawa a Gaza ya yi shahada a hare-haren Isra’ila

Isra’ila ta kwashe kwana 262 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,598 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata

Isra’ila ta kwashe kwana 262 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,598 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,032, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500.

Ma’aikatar kieon lafiya ta Gaza ta ce Isra’ila ta kashe daraktan sashen kula da lafiyar gaggawa na asibitin Gaza.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta tabbatar da kashe Hani Al Jafrawi a harin da jirin yaƙin Isra’ila ya kai.

Sanarwar ta ƙara da cewa “ma’aikatan lafiya na ci gaba da bayar da agajin jinƙai na kwashe mutanen da suka jikkata da waɗanda suka mutu babu dare babu rana, duk da hare-haren da Isra’ila take ci gaba da kai wa”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments