Tattaunawar Musayar Fursunoni Tsakanin Falasdinawa Da Yahudawan Sahayoniyya Ta Rushe

Tattaunawa tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan musayar fursunoni ta fuskanci matsala Tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta

Tattaunawa tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan musayar fursunoni ta fuskanci matsala

Tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto daga wani babban jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Tattaunawa game da yarjejeniyar musanyar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta samu matsala don haka an dakatar da batun tattaunawar a halin yanzu.

Jami’in na haramtacciyar kasar Isra’ila ya kara da cewa: A halin yanzu gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani zabi illa ci gaba da matsin lambar soji don ganin an sakin fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Zirin Gaza.

A wani labarin kuma tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya ce, hanya daya tilo ta dawowar fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Gaza ita ce dakatar da yaki.

Barak ya ce fira minista Benjamin Netanyahu ne ya gaza kuma yake rusa hanya mafi dacewa ga haramtacciyar kasar Isra’ila, don haka ya yi kira da a kawar da shi daga kan mulki ta kowace hanya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da iyalan yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza suke ci gaba da matsin lamba kan neman an kulla yarjejeniyar da zata kai ga sakin ‘yan uwansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments