Kwamitin kula da Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Adadin fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su a Yammacin Kogin Jordan ya karu zuwa 9,325 tun lokacin da aka fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza
Kwamitin da ke kula da fursunonin Falasdinu ya sanar da cewa: Adadin Falasdinawa wadanda aka kama a yammacin gabar kogin Jordan ya kai kimanin 9,325 tun bayan fara kai hare-hare wuce gona da iri kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban bara, bayan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kama wasu Falasdinawa 25 a ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata.
Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kwamitin kula da fursunoni da kungiyar Falasdinawa da aka ‘yantar suka fitar, inda sanarwar ta nuna cewa kamen ya hada dukkan bangarorin al’ummar Falasdinu.
Kamar yadda sanarwar ta kara da cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame akalla Falasdinawa 25 a ranakun Juma’a da Asabar a yankin gabar yammacin kogin Jordan kuma cikinsu har da tsoffin fursunoni.
Har ila yau, sanarwar ta ce an gudanar da kamen ne a tsakanin lardunan Nablus, Tulkaram, Jenin, Ramallah da Khalil. Kwamatin kula da fursunonin ya jaddada matakin ci gaba da musgunawa Falasdinawan da aka kama bayan bude wuta bindiga kan iyalansu da nufin kisa, lamarin da ya lalata gine-ginen Falasdinawa.