Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada Tsakanin Sojojin Sudan Da Dakarun Kai Daukin Gaggawa A El Fasher

Rikicin da ke faruwa a birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa ta kasar Sudan ya lashe rayukan mutane da suka kai 260

Rikicin da ke faruwa a birnin El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa ta kasar Sudan ya lashe rayukan mutane da suka kai 260

A ci gaba da gumurzun da ake yi tsakanin sojojin Sudan da mayakan Dakarun kai daukin gaggawa na rapid support forces a birnin El Fasher fadar mulkin Darfur ta Arewa a tsawon makonni shida a jere, an samu hasarar rayukan mutane da suka kai 260 tare da jikkatan wasu fiye da 1,630 na daban. Kamar yadda kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta tabbatar da hakan a yau Lahadi.

Kungiyoyin kasa da kasa sun bayyana cewa: Kwanaki 9 ke nan da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a kawo karshen fada a birnin El Fasher na kasar Sudan, amma har yanzu ana ci gaba da gwabza fadan.

A ranar 13 ga watan Yuni ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri da ke yin kira ga mayakan dakarun kai daukin gaggawa na rapid support forces da su kawo karshen tashin hankali da kuma killace birnin El Fasher, bayan kada kuri’a kan daftarin kudurin da kasar Birtaniya ta gabatar a kwamitin sulhun, wanda ya kunshi membobin 15, kuma da rinjayen kuri’u 14 ne aka amince da shi, inda Rasha ta ki kada kuri’ar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments