Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh, ya jaddada matsayarsu cewa ƙofarsu a buɗe take game da duk wata tattaunawa da za ta kawo ƙarshen kisan ƙare-dangin da Isra’ila take yi a Gaza idan hakan ya dace da buƙatunsu.
Haniyeh ya bayyana haka ne a wata lacca a birnin Beirut inda aka tattauna game da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza.
Shugaban Hamas ya ce a shirye ƙungiyarsu take ta bayar da haɗin kai game da “duk wata yarjejeniya ko tsari da zai tabbatar da matsayarmu a tattaunawar tsagaita wuta.”
Ya jaddada matsayar Hamas ta kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, da janyewar Isra’ila daga yankin da sake gina shi da kai kayan agaji da kuma yin musayar fursunoni.