Iran Ta Ja Kunnen Isra’ila Game Da Kaddamar Da Yaki Kan Hizbullah

Iran ta gargadi Isra’ila game da illar da ke tattare da kaddamar da yaki na bai daya a kan kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Iran ta gargadi Isra’ila game da illar da ke tattare da kaddamar da yaki na bai daya a kan kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta fada a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a cewa Isra’ila za ta zata zamo mai hasara ” kan duk wani matakin soji kan Lebanon.

“Ba shakka, Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon tana da karfin kare kanta da kuma kasar Lebanon-watakila lokacin da za a kawar da wannan gwamnati ne ma ya zo,” in ji tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya.

Har ila yau, Iran ta yi gargadin cewa duk wani mataki da Isra’ila za ta dauka kan Lebanon, ka iya jefa yankin cikin wani sabon rikici.

Sanarwar ta kara da cewa, “Duk wani matakin da bai dace ba da gwamnatin Isra’ila ta dauka na iya jefa yankin cikin wani sabon yaki.

Gwamnatin Isra’ila da kungiyar Hizbullah na musayar wuta a kan iyakar kudancin kasar ta Lebanon kusan a kowace rana tun lokacin da aka fara kai farmakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba.

Rikicin ya zafafa a makon da ya gabata musamman bayan da Isra’ila ta kashe wani babban kwamandan kungiyar Hizbullah.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta amince da shirin kai hari kan kasar Labanon, lamarin da ke kara nuna fargabar cewa gwamnatin kasar na iya yin barazanar cewa za ta mayar da Lebanon wata Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments