Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Naseer Kan’ani ya bayyana cewa matakan da kasar Canada ta dauka kan dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wato (IRGC) khidima ce babba ga HKI a lokacinda take kissan kare dangi a kasar Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Naseer Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa ba abin mamaki bane idan kasar Canada ta sanya dakarun juyin juyahalin musulunci na kasar Iran cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta.
A ranar laraban da ta gabata ce ministan tsaron cikin gida na kasar Canada Dominic Lublone ya bada sanarwan cewa majalisar dokokin kasar Canada ta amince da bukatar gwamnatin kasar na Sanya dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran a matsayin kungiyar -abinda Yakira- yan ta’adda.
A nashi bangaren mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ya bayyana matakin da gwamnatin kasar Canada ta dauka kan dakarun IRGC a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma bai da wani tasiri a ayyukan IRGC a ciki da wajen kasar.